Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta yi watsi da zargin Isra'ila akan Falasdinu

Ministan harkokin wajen Faransa  Jean-Marc Ayrault da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu Reuters/路透社

Gwamnatin Faransa ta yi watsi da zargin da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi wa kasar na goyan bayan Falasdinawa akan shirin sasanta rikicinsu da Israila da take shiryawa.

Talla

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Marc Ayrault ne ya yi watsi da furucin na  Netanyahu wanda ke zargin cewar goyan bayan da Faransa ta bai wa hukumar UNESCO wadda ta amince da halarcin Falasdinu, nuna kiyayya ce ga Israila.

Ministan ya ce Faransa bata da wata manufa ta dabam, sai dai bukatar ganin an sasanta matsalar da kuma tabbatar da cewar kungiyar mayakan ISIS bata samu damar shiga yankin ba.

Ayrault ya ce Faransa za ta ci gaba da taka rawa wajen ganin an samo masalaha kan takaddamar da ke tsakanin Yahudawa da Falasdinawa bayan ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu da shugaba Mahmud Abbas.

Shi dai Netanyahu ya bayyana cewar, matsayin Faransa a hukumar UNESCO ya nuna cewar ta zabi bangare a yunkurinta na sasanta rikicin gabas ta tsakiya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.