Isa ga babban shafi
Yemen

'Yan Tawayen Yemen Sun Saki Mutane 276

Wani yaro ya yi nasarar samun kayan abinci na agaji a Yemen
Wani yaro ya yi nasarar samun kayan abinci na agaji a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah

‘Yan tawayen Shia na Houthi a kasar Yemen sun sanar da sakin wasu mutane 276 magoya bayan Gwamnati da ake tsare da su na tsawon watanni.

Talla

Shafin ‘yan tawayen na Yanar Gizo na cewa mutane 200 suka saki a garin Rada dake tsakiyar gunduman Baida, sannan kuma aka saki wasu mutane 76 daga gunduman Dhamar.

Su mutane 200 da aka saki a garin Rada an tsare su ne saboda zargin suna neman bada goyon baya ga sojan karo-karo na kasashen Larabawa dake yakar ‘yan tawayen, yayinda mutane 76 da aka saki daga Dhamar an tsare su ne saboda zargin suna baiwa Gwamnatin kasar hadin kai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.