Isa ga babban shafi
Bahamas

Bahamas ta gargadi ‘yan kasarta zuwa Amurka

Firaministan Bahamas Perry Gladstone Christie
Firaministan Bahamas Perry Gladstone Christie bahamaspress

Gwamnatin kasar Bahamas ta yi gargadi ga ‘Yan kasarta su yi hankali da rayuwarsu a yayin da suke shirin zuwa Amurka saboda matsalar wariyar launin Fata da 'Yan Sanda fararen fata ke harbe bakake.

Talla

Yawancin dai mutanen Bahamas Bakaken fata ne, kuma tashin hankalin da ake yi a Amurka barazana ne ga rayuwarsu.

Ma’aikatar harakokin wajen Bahamas da ta fitar da gargadin tace ‘yan kasar su yi taka-tsan tsan ga duk wata mu’amula da ta hada su da ‘Yan sandan Amurka.

Gobe litinin dai ranar hutu ce a Bahamas kuma ana tunanin ‘yan kasar za su yi amfani da dogon hutun domin zuwa Amurka.

Rikici dai na neman kazancewa a Amurka sakamakon harbe wasu bakaken fata da ‘Yan sanda fararen fata suka yi .
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.