Isa ga babban shafi
Amurka

Clinton za ta haifar da yakin duniya-Trump

Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat
Donald Trump na Republican da Hillary Clinton ta Democrat REUTERS/Carlos Barria

Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam’iyyar republican Donald Trump ya ce manufofin kasashen waje na abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton ta Democrat, za su haifar da yakin duniya na 3 a Syria.

Talla

Trump ya maida martini kan bukatar da Clinton ta gabatar ta iyakance shawagin jiragen sama a sararin samaniyar Syria mai fama da tashe-tashen hankula, matakin da wani babban jami'in sojin Amurka ya ce, zai haddasa rikici da jiragen saman Rasha.

Mrs. Clinton ta caccaki Trump kan rashin daukar barazanar da Amurkawa ke fuskanta da muhimmaci.

A cewar Mr, Trump, ya  kamata Amurka ta maida hankali kan yadda za ta murkushe mayakan IS a maimakon kokarin hambarar da shugaban Syria Bashar Al Assad.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.