Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Putin ya nisanta kanshi da siyasar Amurka

Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka
Shugaban Rasha, Vladmir Putin da Barack Obama na Amurka REUTERS

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi watsi da zargin da ake wa kasar shi na kokarin yin katsalandan ga harakokin siyasar Amurka tare da yin kutse ta barauniyar hanya ga shafukan intanet na yakin neman zaben Hillary Clinton.

Talla

Bagaren Jam’iyyar democrat da ke mulki a Amurka ne ke zargin Rasha da marawa Donald Trump baya musamman irin kalaman yabon Putin da ke fitowa daga bakin dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Republican.

Amma Shugaba Putin a lokacin da ya ke ganawa da masana kimiyar siyasa a Sochi, ya ce kamar ciwon hauka na cikin matsalolin Amurka, a cewar shi ba zai iya tuna wata Kalmar da ta fi dacewa dangane da zargin tasirin Rasha a zaben Amurka ba.

Putin ya ce yana mamakin yadda wasu ke tunanin Rasha na iya tasiri ga zabin Amurkawa, domin Amurka ba karamar kasa bace.

A makon jiya ne dai gwamnatin Amurka ta zargi gwamnatin Rasha da kokarin yin katsalandan ga zaben shugaban kasa tare da shiga ta barauniyar hanya ga shafukan wasu cibiyoyin siyasar kasar.

Rasha kuma ta musanta zargin, inda Shugaba Putin ya ce wannan dubaru ne na karkatar da hankalin Amurkawa daga matsalolin da suka dame su na cikin gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.