Isa ga babban shafi
UNESCO

Kasashe ba su damu da kisan ‘Yan jarida ba- UNESCO

UNESCO ta bukaci kawo karshen kisan 'Yan jarida a duniya
UNESCO ta bukaci kawo karshen kisan 'Yan jarida a duniya Eddie Gerald / Getty Images

Wani rahoto da hukumar UNESCO ta fitar ya ce a cikin shekaru 10 da suka gabata, akalla ‘yan jaridu 827 ne sura rasa rayukansu a sassa daban daban na duniya. Rahoton ya yi kira ga kasashen duniya su dauki matakan kawo karshen kisan ‘Yan Jarida.

Talla

UNESCO ta wallafa rahoton ne bayan tattara alkaluma akan ‘yancin aikin jarida a duniya, musamman a game da yawan ‘yan jaridar da suka rasa rayukansu tsakanin 2014-2015.

A kasashen Larabawa kawai an samu asarar rayukan ‘Yan Jarida 41 a 2014 yayin da aka kashe 37 a 2015, kamar yadda rahoton ya ce an kashe wasu ‘yan jaridun 26 a 2014 a Latin Amurka tare da kashe wasu 25 a baya.

Rahoton ya ce a nahiyar Afirka an kashe ‘yan jarida 11 a 2014 yayin da aka kashe 16 a shekarar bara. To sai dai yayin da ma’aikatan yada labarai 12 suka rasu a 2014 a yankin Asiya, shekarar da ta biyo baya ta yi muni tare da kashe akalla 22.

A dunkule dai rahoton na nuni da cewa ‘yan jarida 98 ne suka mutu akan aikinsu a 2014, inda aka kashe 115 a shekarar bara a sassa daban daban na duniya.

An wallafa rahoton ne kafin yau da aka ware a matsayin ranar yaki da cin zarafin ‘Yan Jarida a duniya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.