Isa ga babban shafi
Pakistan-Afghanistan

Mutane 10 sun mutu a Pakistan saboda zabtarewar kankara daga tsaunuka.

Dusar kankara da tayi taadi a shekara ta 2010 inda mutane 160 suka mutu a tsakanin Afghanistan da Pakistan..
Dusar kankara da tayi taadi a shekara ta 2010 inda mutane 160 suka mutu a tsakanin Afghanistan da Pakistan.. AFP PHOTO/SHAH Marai

Mutane akalla 10 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon iska da ruwan sama da ambaliyar dusar kankara daga tsaunukan dake dab da wasu kauyuka kasar Pakistan.

Talla

Wasu mutanen akalla ana ta neman inda suka bace a masifar da ta auku a kauyukan dake kan iyaka na arewacin Pakistan da kasar Afghanistan.

Dusar kankara yanzu haka ta rufe sassa da dama na kasar Afghanistan musamman yankun  gunduman Badakhashan inda cikin kwanaki biyu aka ce mutane 19 suka gamu da ajalin su, wasu mutane 17 kuma suka sami munanan raunuka.

Cikin mamatan a yankin Pakistan akwai mata hudu da yara kananan hudu.

Yankin ya sha fuskantar ambalisar kankara dan tsakanin nan.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.