Isa ga babban shafi
Colombia

Colombia na tattaunawa da 'yan tawayen ELN

Wasu daga cikin 'yan tawayen ELN na Colombia
Wasu daga cikin 'yan tawayen ELN na Colombia AFP

Hukumomin Colombia sun fara tattaunawa da ayarin kungiyar ‘yan tawaye na karshe da ake kira National Liberation Army ELN, a kokarin ganin an kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru 53 ana fafatawa wanda ya kai ga kashe mutane akalla dubu 260.

Talla

Juan Mariguet wakili na kasar Equador da ke karbar bakwancin sulhun ya ce, bangarorin biyu na bukatar ganin an samu dauwamammiyar zaman lafiya a Colombia.

Wannan sulhu da ayarin ‘yan tawayen na karshe, zai kawo karshen fafutukar da shugaba Juan Manuel Santos ke yi na wanzar da zaman lafiya bayan nasarar da aka samu wajen sulhu da babbar kungiyar ‘yan tawayen FARC.

Sai dai kwararru sun gargadi cewa, cimma yarjejeniya da ELN zai fi wahala fiye da yadda gwamnatin Colombia ta cimma yarjejeniya ta 'yan tawayen FARC.

Amma hakan bai sanyaya gwiwar shugaba Santos ba dangane da shiga tattaunawa da 'yan tawayen na ELN.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.