Isa ga babban shafi
Vatican

Trump ya gana da Fafaroma Francis

Fafaroma François tare da shugaban Amurka Donald Trump a fadar Vatican.
Fafaroma François tare da shugaban Amurka Donald Trump a fadar Vatican. REUTERS/Alessandra Tarantino

Shugaban mabiya darikar Katolika Fafaroma Francis ya bukaci shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da shugabancinsa domin tabbatar da zaman lafiya a duniya a lokacin ganawa ta farko a tsakaninsu, a ziyarar da Trump ya kai a fadar Vatican.

Talla

A lokacin ganawar, shugaban na Vatican ya bukaci Trump da ya yi kokarin samar da zaman lafiya a duniya, shawarar da shugaban na Amurka ya ce zai yi amfani da ita.

Cikin minti 30 Trump da Fafaroma Francis suka yi ganawar ta keke da keke, kuma dukkaninsu sun ce sun yi tattaunawa mai matukar muhimmaci.

Batun adawa da zubar da ciki da kisan Kiristoci a yankin gabas ta tsakiya na daga cikin batutuwan da suka tattauna. Amma tsakaninsu babu wanda ya bayyana cewa sun tabo batun ‘yan gudun hijira da matsalar canjin yanayi da sauran batutuwan da suke da sabani da juna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.