Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya fasa mayar da ofishin jekadancin Amurka zuwa birnin Kudus

REUTERS/Amir Cohen

Shugaban Amurka Donald Trump ya sauya ra’ayi kan dauke ofishin jekadancin Amurka daga Tel Aviv babban birnin Isra’ila zuwa Jerusalem, matakin da ake ganin zai taimaka ga alkawarin Trump na farfado da tattaunawar sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinawa

Talla

Kodayake wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya tabbatarwa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa Trump ya jinkirta daukar matakin ne da nufin samar a zaman lafiya a rikicin gabas ta tsakiya.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana rashin jin dadin jinkirta matakin na Amurka, duk da cewa sun fahimci juna da Trump a ziyarar da ya kai a Isra’ila a makon jiya.

Tun a lokacin yakin neman zabensa, Donald Trump ya yi alkawalin dauke ofishin jekadancin Amurka daga Tel Aviv zuwa birnin Kudus, wanda ya danganta zai kasance a matsayin babban birnin Isra’ila da Falasdinawa.

A ziyarar farko da ya kai a Isra’ila da yankin Falasdinawa Trump ya yi alkawalin sasanta rikici tsakanin bangarorin biyu ba tare da ya yi allawadai da gine ginen da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankunan Falasdinawa ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.