Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya bukaci Kasashen Larabawa sun sassanta kan su

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci sassanta rikicin kasashen larabawa da Qatar
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci sassanta rikicin kasashen larabawa da Qatar REUTERS/Charles Platiau

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya bukaci shugabannin kasashen Saudi Arabia da Iran da Qatar da su tattauna a tsakanin su dan kawo karshen tankiyar da aka samu wadda ke neman raba kan su.

Talla

Shugaba Macron wanda ya yi Magana ta waya da Sarki Salam bin Abdulaziz na Saudi Arabia da Sheik Tamim bin Hammad Al Thani na Qatar da kuma shugaba Hassan Rouhani na Iran ya bukaci su hada kan su ta hanyar tattaunawa domin magance barakar da aka samu.

Shugaban na Faransa ya jadada muhimmanci zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma yaki da ta’addanci domin murkushe daukacin 'yan ta’adda.

Shi ma Donald Trump na Amurka ya yi Magana da shugabanin Qatar da Saudiya inda ya bayyana aniyar sa ta shiga tsakani.

Tuni Sarkin Kuwait Sheikh Sabah Al Ahmad al-Sabah ya fara ziyarar kasashen da rikicin ya shafa domin ganin an samu fahimtar juna domin kawo karshen matsalar.

A bangare daya kuma Majalisar kasar Turkiya ta bada umurnin girke sojojin kasar a Qatar domin kaucewa duk wata barazana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.