Isa ga babban shafi
Qatar

Qatar ta yi watsi da takunkumin da aka sanya ma ta

Ministan Harkokin Wajen Qatar Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani tare da  Serguei Lavrov a birnin Moscow na Rasha
Ministan Harkokin Wajen Qatar Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani tare da Serguei Lavrov a birnin Moscow na Rasha Yuri KADOBNOV / AFP

Kasar Qatar ta yi watsi da abin da ta kira haramtaccen takunkumin da Saudi Arabia da kawayenta suka kakaba ma ta sakamakon rashin fahimtar junan da suka samu.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman al-Thani ya bayyana haka a yayin wata ziyarar da ya kai a kasashen Birtaniya da Faransa domin yi wa shugabani bayanin assalin abin da ke faruwa.

Ministan ya ce, babu wata kasa da ta ke da hurumin tilasta wa kasarsa manufofinta na kasashen waje, in da ya ke cewa a shirye suke su tattauna akan turba mai kyau don warware matsalar amma ba katsalandan kan harkokin kasar ba.

Saudi Arabia da Daular Larabawa da Bahrain da Masar sun janye jakadunsu daga Qatar tare da katse hulda da ita saboda zargin da su ke ma ta na goyan bayan ayyukan ta’addanci.

Daga cikin zargin har da taimaka wa kungiyar Hamas ta Falasdinawa mai gwagwarmayar neman yancin Falasdinu, zargin da Qatar ta ki amincewa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.