Isa ga babban shafi
Amurka

An Kammala Gasan Karnuka mafiya Muni Na Duniya

Martha Karya mafi muni a duniya wadda ta lashe gasan shekara ta 2017
Martha Karya mafi muni a duniya wadda ta lashe gasan shekara ta 2017 USA TODAY

An kammala bukin shekara-shekara na bana na karnuka da suka fi muni a duniya wanda aka yi a kasar Amurka inda wata karya mai suna  Martha ta yi nasarar zama karya mafi muni yanzu haka a doron kasa.

Talla

Wannan dai shine karo na 29 da ake nada kare ko karya duk shekara dake da munin tsiya a fadin duniya.

Leben sama na wannan karya, ya zubo kasa ya rufe leben kasa, yayinda hatta idanunta ba’a iya gani saboda naman fuskan,  da harshen ta sun zazzago kasa.

Tsaban kudin Amurka Dala Dubu kusan biyu da kulawa ta musamman na tsawon wani lokaci da wasu kyautuka ake baiwa kare ko mkarya da ta lashe bukin nuna munin.

Sabuwar karyan mai muni na duniyaza'a bata kyauta na alfarma sannan  za'a kuma kwashe ta domin kaita yawo wurare daban-daban a New York.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.