Isa ga babban shafi
Koriya-Amurka

Moon Jae-In ya ce babu wani yakin da za a gwabza a Yankin su

Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In
Shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In Reuters/路透社

Shugaban Kasar Koriya ta Kudu Moon Jae-In ya ce babu wani yakin da za a gwabza a Yankin su, domin kasar sa ke da hurumin bada umurni ga sojojin Amurka na mayar da martini kan duk wata takala daga koriya ta Arewa.

Talla

Yayin da ya ke ganawa da manema labarai kan cika kwanaki 100 a karagar mulki, shugaban ya ce ba za su bari a lalata kasar su ba, bayan wahalar da suka yi wajen sake gina ta daga yakin da suka gwabza da Koriya ta Arewa.

Shugaba Moon ya ce babu wani wanda ya ke da hurumin daukar matakin fara yaki ba tare da amincewar Koriya ta Kudu ba.

Kalaman Moon na zuwa ne bayan sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya gabatar da kan sa a matsayin wanda zai jagoranci sasanta rikicin diflomasiya tsakanin Koriya ta Arewa da Amurka, inda ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen tankiyar da ake samu.

Guterres ya shaidawa manema labarai cewar, ganin yadda hankali ya tashi, ya zama wajibi ofishin sa ya bada gudumawa wajen ganin ba a samu aiwatar da abinda za a yi nadama a kai ba.

Sakataren ya ce zai ci gaba da tintibar bangarorin da ke cacar-bakin domin ganin an shawo kan matsalar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.