Isa ga babban shafi
Amurka

Kotun Amurka ta amince da dokar hana shigar baki

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Carlos Barria

Kotun kolin Amurka ta bai wa shugaba Donald Trump damar aiwatar da dokarsa ta hana baki shiga cikin kasar daga kasashen duniya.

Talla

Alkalan kotun sun amince da bukatar gwamnatin Trump ta soke hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke a can baya, in da ta yi watsi da matakin shugaban na hana shiga baki shiga cikin Amurka.

Gwamnatin Trump ta nuna fargabar cewa, hukuncin kotun daukaka karar zai bai wa wasu bakin haure kimanin dubu 24 damar shiga kasar.

Sai dai sabon hukuncin da kotun kolin ta yanke na a matsayin kwarya-kwaryar nasara ga shugaba Trump kafin nan da watan Oktoba mai zuwa, lokacin da babbar kotu za ta kammala zaman sauraren wata kara ta daban kan ingancin takardar umarni da Trump ya sanya wa hannu don haramta kasashen Musulmi 6 shiga cikin Amurka.

Kasashen sun hada da Iran da Libya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.