Isa ga babban shafi

Kasashen Musulmi sun lashi takobin murkushe 'yan ta'adda

Yarima Mohamed bin Salmán
Yarima Mohamed bin Salmán REUTERS/Hamad I Mohammed

Kasashen Musulmi 40 karkashin jagorancin Saudiya sun lashi takobin kawo karshan ta’addanci a duniya, a wani taro da suka gudanar a birnin Riyadh.

Talla

Yarima Mohammed bin Salman na Saudiya da ke jagoranci taron a mastayin Ministan tsaron kasar, ya ce rashin hadin-kan kasashen ya bai wa ‘yan ta’adda daman kasancewa barazanar a garesu.

Sai dai yarjejeniyar da suka cim-ma a fani Soji da kudadde da bayanan sirri da kuma siyasa zai kawo karshan ayyukan ta’addanci, inji Yarima Salman.

Taron shi ne irinsa na farko na ministocin tsaro da manyan jami’ai daga kawance kasashen Musulmi da ke yakar ta’addanci, da a hukumance su 41 ne ke gudanarwa.

Sai dai taron bai gayyaci kasar Iran da Syria da Iraqi ba.

A shekara ta 2015 aka kafa kawancen, karkashin jagoranci Yarima Salman, wanda nada shi a matsayin magajin sarautar Saudiya ya sauya siyasar kasar.

Tattaunawar na wannan lokaci ya zo ne yayin da rikici ke sake tsananta tsakanin Riyadh da Tehran, musamman saboda yakin Syria da Yemen da kuma halin da ake ciki a Lebanon.

Saudiya na ci gaba da zargin Iran da taimakawa mayaka a gabas ta tsakiya, ciki hadda kungiyar Hezbollah da Shi’a a Lebanon da Huthi a Yemen.

Kazalika tattaunawar na zuwa ne yayin da sojojin kawance da dama, ciki hada wadda Iran ke goyon baya, da Saudiya da Amurka ke nazarin hanyoyin dakile mayakan IS daga maboyansu na karshe a Iraq da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.