Isa ga babban shafi
Amurka

Amurka ta ce IS barazana ce har yanzu

Iraki na ikirarin cewa ta gama da mayakan IS a kasar.
Iraki na ikirarin cewa ta gama da mayakan IS a kasar. REUTERS/Stringer

Amurka ta yi gargadin cewa har yanzu kungiyar IS barazana ce ga zaman lafiya duk da tabbacin da firaministan kasar Iraqi ya yi kan cewa sun kawar da kungiyar daga kasar.

Talla

A cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta kasar Amurka Heather Naurt, ya kamata a sanya ido sosai wajen magance duk wani tsattsauran ra’ayi domin kauce ma yiwuwar dawowar IS ko kuma wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sai dai Amurka din ta yaba da kawo karshen mamayar da kungiyar ta yi a kasar ta Iraqi.

Naurt ta ce bayanin na Firaministan Iraqi ya nuna karshen kungiyar, tare kuma da ‘yanta mutanen da ke yankunan da a baya kunigiyar ta kame daga mulkin kama-karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.