Isa ga babban shafi
Afrika

Mayakan ISIS dubu 6 za su koma Afrika- AU

Mayakan ISIS a Raqa
Mayakan ISIS a Raqa © REUTERS/Stringer

Kungiyar Kasashen Afrika AU ta yi gargadin cewar akalla mayakan ISIS 6,000 ake fargabar cewa za su koma nahiyar Afrika bayan an yi nasarar murkushe su a kasashen Iraqi da Syria.

Talla

Kwamishinan tsaro da zaman lafiya na AU Smail Chergui ya ce, ya zama dole kasashen Afrika su hada kansu wajen aiki tare da kuma musayar bayanan sirri domin kauce wa barazanar da irin wadannan mayaka ke tattare da ita.

Kwamishinan ya ce, suna da bayanan da ke nuna musu cewar, daga cikin mayakan ISIS dubu 30, ‘yan kasashen waje da suka shiga kungiyar ‘yan ta’adda a Gabas ta Tsakiya, sun kai 6,000 kuma sun fito ne daga kasashen Afrika.

Mayakan daga kasashen ketare sun yi mubaya'a ga kungiyar ISIS ne bayan ta samu nasarar karfe wurare da dama a Iraqi da Syria a shekara 2014.

Sai dai dakarun kasashen tare da taimakon rundunar hadaka sun yi nasarar fatattakar mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.