Isa ga babban shafi
Australia

Wani mai mota ya buge mutane 'da gangan' a Australia

'Yan sanda sun ce sun damke direban motar da ta buge mutane 2 a Melbourne.
'Yan sanda sun ce sun damke direban motar da ta buge mutane 2 a Melbourne. AAP/Joe Castro via REUTERS

Ƴan sanda a ƙasar Australia sun ce wani mutum da ya kutsa cikin jama'a da motarsa a Melbourne, birni na biyu mafi girma a ƙasar, ya yi haka ne da gangan.

Talla

Ƴan sandan sun ruwaito cewa wata ƙaramar mota ta afka wa matafiya a ƙafa a wata mahaɗa mai yawan hada-hadar jama'a da ke tsakiyar birnin.

Al'amarin dai ya yi sanadiyyar raunata mutane guda 14, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke cikin mawuyacin hali.

Mai magana da yawun ƴan sanda a yankin Victoria, Russell Barrett ta faɗi wa manema labaru cewa ya zuwa yanzu ba su san dalilin da ya sa mutumin ya aikata hakan ba.

Ƴan sandan sun ce sun kama mutane biyu dangane da al'amarin, daga cikin su har da direban motar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.