Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya

Amurka ta yaba da rage kasafin kudin Majalisar Dinkin Duniya

Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley yayin amsa tambayoyin manema labarai a birnin New York.
Jakadiyar Amurka a zauren Majalisar Dinkin Duniya Nikki Haley yayin amsa tambayoyin manema labarai a birnin New York. Drew Angerer / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

Amurka ta bayyana jin dadi kan matakin zaftare dala miliyan 285, daga kasafin kudin Majalisar Dinkin Duniya na ayyukan yau da kullum.

Talla

Matakin ya zo ne, bayanda babban taron Majalisar ya amince da kasafin dala biliyan 5.3 a maimakon sama da dala biliyan 5.4.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Nikki Haley ta ce an zartar da matakin zaftare kasafin kudin Majalisar a lokacin da ya dace, idan aka yi la’akari da yadda ake almubazarranci da kudaden Majalisar ba kuma tare da an cimma nasarorin da ake bukata ba.

Kasar Amurka ce dai ke kan gaba wajen bai wa majalisar dinkin duniya gudunmawar kudade, inda take samar da kashi 22 na kasafin kudin Majalisar ita kadai.

Kasafin kudin ayyukan yau da kullum na Majalisar Dinkin Duniya, ya banbanta da kasafinta kan tafiyar da ayyukan dakarunta na wanzar da zaman lafiya da ke sassan duniya, wanda shi ma a wannan shekara ta 2017 aka zaftare dala miliyan 600 daga cikinsa.

A watan Satumban da ya gabata ne, Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Majalisar Dinkin Duniya da gazawa wajen kyakkyawan jagoranci, sakamakon sabawa ka’idojin aiki da barnatar da kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.