Isa ga babban shafi
Duniya

Duniya za ta fuskanci barazana a 2018-MDD

Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres. REUTERS/Mike Segar

Yayin da ake shirye-shiryen shiga sabuwar shekara ta 2018, sakatare-janar na majalisar ɗinkin duniya Antonio Guterres ya ce duniya na fuskantar mummunar barazana.

Talla

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr Guterres ya ce rikice-rikice sun rincabe, haɗurra sun ƙaru, sannan barazana game da yaɗuwar makaman ƙare-dangi ta yi zafi mafi muni cikin shekarun nan.

Sanarwar ta ƙara da cewa duniya na fuskantar gagarumin take haƙƙokin bil’adama da rarrabuwar kawuna.

A saboda haka ne shugaban na majalisar ɗinkin duniya ya yi kira da a haɗa kai domin ganin yadda za ciyar da duniya gaba da kuma zamowa mafaka ga dukkanin bil’adama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.