Isa ga babban shafi
Amurka-Turkiyya

Akwai yiwuwar arangama tsakanin sojin Amurka da na Turkiyya

Shugaban kasar Amurka Donald Trump da na Turkiyya Raceb Tayyib Erdogan.
Shugaban kasar Amurka Donald Trump da na Turkiyya Raceb Tayyib Erdogan. REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaban Amurka ya gargadi Turkiyya da ta janye ayyukan sojojinta daga Syria domin kauce ma yiwuwar taho-mu-gama tsakanin sojojin nata da dakarun Amurka da ke ƙasar.

Talla

Ita dai Turkiyya na kai farmaki ne ta sama da ta ƙasa a kan mayaƙan Ƙurdawa masu samun goyon bayan Amurka, waɗanda Turkiyya ke yi wa kallon masu goyon bayan Ƙurdawa da suka kwashe shekaru suna yi wa gwamnatin Turkiyya tawaye.

A lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya tattauna da takwaransa na Turkiyya Raceb Erdogan ta waya, ya buƙaci Turkiyya ta sassauta hare-haren da take kai wa a ƙasar ta Syria.

Amurka dai tana da sojoji waɗanda suka kai 2000 a ƙasar Syria.

Sai dai majiyoyi daga gwamnatin Turkiyya sun ce bayanin da Amurka ta fitar bai yi daidai da abubuwan da shugabannin ƙasashen biyu suka tattauna ta waya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.