Isa ga babban shafi
Amurka-Falasdinu

Amurka za ta katse tallafinta a Falasdinu saboda Isra'ila

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Kevin Lamarque

Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar katse tallafin da kasar ke bai wa Falasdinu muddin ta ki shiga tattaunawar sulhu da Isra’ila, tare da bayyana cewa yankin ya yi kunan-shegu da tattaunawa da mataimakinsa a ziyarar da ya kai gabas ta tsakiya.

Talla

Mista Trump da ke bayyana hakan bayan tattaunawa da Friministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a taron tattalin arziki na Davos ya ce, manufarsa ita ce samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

A cikin wannan watan Falasdinu ta nuna halin ko-in-kulla a ziyarar da Mataimakin shugaban Mike Pence ya kai yankin gabas ta tsakiya, wanda a cewar shugaban rashin biyayya ne, don haka Amurka ba za ta bai wa kasar tallafi ba har sai ta amince da sulhun.

Trump ya ce gwamnatinsa ta shirya daftarin sulhu na musamman kuma ci gaba ne ga Falasdinu domin yana kunshe da batutuwa da dama da aka shafe tsawon shekaru ana tattaunawa da neman yardarsu.

Shugaban ya kuma kara da cewa bayyana kudus a matsayin birnin Isra’ila na daga cikin tsarin sulhun kasar, kuma Isra’ila za ta biya, domin za suyi abin da zai kasance mai kyau sosai, sai dai shugaban bai yi karin haske kan abin da ya ke nufi ba.

A farkon bude taron tattalin arzikin na Davos, Sarki Abdullah na Jordan ya ce, Kudus na daga cikin abubuwan da zai kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.