Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta kulla cinikayyar Dala biliyan 16 da UAE

Samfurin jirgin saman Airbus da Faransa ta cimma yarjejeniya da Daular Larabawa akan Dala dala biliyan 16
Samfurin jirgin saman Airbus da Faransa ta cimma yarjejeniya da Daular Larabawa akan Dala dala biliyan 16 @Airbus SAS

Firaministan Faransa Edouard Philippe ya jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar sayar da wasu jiragen jigilar fasinja samfurin Airbus A380 na kimanin Dala biliyan 16 ga birnin Dubai da ke Hadaddiyar Daular Larabawa.

Talla

Yarjejeniyar wadda Sheikh Ahmad Sa’eed Al Maktoum, shugaban kamfanin sufurin jiragen sama na Emirates tare da Mikhail Houri jagoran kula da harkokin kamfanin a yankin gabas ta tsakiya suka sanya wa hannu, sun ce za ta kara bunkasa harkokin zirga-zirga a kasar.

Ko a cikin watan Disambar, Emirates ya amince da sayen wasu jirage 20 tare da bukatar kara wasu 16 kwanaki kalilan bayan kamfanonin kera jirage na Turai sun yi shelar dakatar da aiki idan har ba a samu masu saye ba.

Sai dai kuma wasu na ganin yarjejeniyar abar tambaya ce ga birnin na Dubai, la’akari da yadda ya amince da sayen kimanin jirage arba’in na kamfanin Boeing kan kudi fiye da Dala biliyan 15.

Filin jirgin saman Dubai dai shi ne filin jirgi mafi yawan hada-hadar fasinja a shekarar 2017, in da a kusan shekaru 4 da suka gabata yake daukar akalla matafiya miliyan 88 da dubu 200.

Wani babban jami’i da ke cikin tawagar ta Faransa ya shaida wa manema labarai cewa yarjejeniyar za ta tallafa wa kamfanin Airbus ci gaba da kirar jiragen samfurin A380.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.