Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya nada mai tsattsauran ra'ayi don ba shi shawara

Sabon mai bai wa Trump shawara kan harkokin tsaro, John Bolton
Sabon mai bai wa Trump shawara kan harkokin tsaro, John Bolton REUTERS/Mike Segar/File Photo

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da nada John Bolton, wani mai tsattsauran ra’ayi a matsayin sabon mai ba shi shawara kan harkokin tsaro domin maye gurbin Janar HR McMaster.

Talla

Ministocin Isra'ila sun bayyana farin cikinsu da nadin Bolton, mutumin da aka bayyana shi a matsayin mai goyan bayan kasar, yayin da aka rawaito shi a baya yana bayyana mutuwar shirin kafa kasar Falasdinu.

Kungiyar Falasdinu ta ce, nadin Bolton wata alama ce da ke nuna matsayin Amurka na kauce wa warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kazalika  an bayyana sabon mai bada shawaran a matsayin babban makiyi ga kasar Iran da ke kan gaba wajen nuna adawa ga Yahudawa.

Shugaba Trump dai na ci gaba da nada gaggan abokan Isra'ila a mukamai a manyan mukamai daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.