Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen Turai sun mara baya ga Amurka don kai farmaki Syria

Wani yanki a Syria bayan luguden wuta kan 'yan tawaye.
Wani yanki a Syria bayan luguden wuta kan 'yan tawaye. REUTERS/Bassam Khabieh

A dai dai lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ke ikirarin kai hari da makami mai linzami Syria don maida martini saboda amfani da makamai masu guba, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bada tabbacin cewa suna da kwararan hujjoji kan amfani da nau'ikan makaman a Syria.

Talla

A jawaban da shugaban Amurkan Donald Trump ya gabatar ya ce martanin Amurka na iya zuwa kowane lokaci daga yanzu.

Ko da ya ke dai a bangare guda itama Rashan ta sha alwashin kakkabo duk wani makami mai linzami da aka chilla zuwa Syria.

Shima dai shugaban Faransa Emmanuel Macron a bangare guda yayin wata hira da shi a yau, ya ce Faransa na da kwararan hujjoji da ke nuna anyi amfani da makamai masu guba a Syria.

Ita kuwa Firaministar Birtaniya Theresa May na shirin wani taron gaggawa ne na mazalisar zartaswa a kasar sakamakon rade-radin cewa an gaza sanin matsayin kasar dangane da shirin Amurka na kai farma Syria da makami mai linzami.

A bangare guda Itama shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel cewa ta yi hakan na nufin cewa Syria ba ta lalata dukkan makamanta masu guba ba kamar yadda ta sanar a baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.