Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Macron ya shawo kan Trump kan janye dakarunsa daga Syria

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump
Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwaransa na Amurka Donald Trump LUDOVIC MARIN / AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewar shi ya shawo kan shugaba Donald Trump wajen ganin ya bar sojojin Amurka a kasar Syria domin ci gaba da gudanar da ayyukansu.

Talla

Kwana guda bayan Faransa ta bi sahun Amurka da Birtaniya wajen kai hare-hare cikin Syria, shugaba Macron ya bayyana cewar hare-haren sun halatta, in da ya bukaci kasashen duniya su ci gaba da matsin lamba ta hanyar diflomasiya wajen kawo karshen yakin da aka kwashe shekaru 7 ana fafatawa.

Shugaban na Faransa ya ce, ba wai sun kaddamar da yaki da shugaba Bashar al Assad ba ne, sai dai gargadi ne a gare shi cewar, ba za su amince da amfani da makami mai guba kan fararen hula ba.

Macron ya ce, an kai hare-haren ne kan wuraren da ake kera makaman masu guba, kuma sun samu nasara.

Sai dai bayan yada kalaman na shugaba Macron, mai magana da yawun fadar shugaban Amurka, Sarah Sanders ta ce, har yanzu matsayin kasar bai sauya ba na shirin janye dakarun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.