Isa ga babban shafi
Isra'ila

Isra'ila ta dakatar da shirin korar bakin haure 'yan Afrika

Kafin dakatar da shirin dai Isra'ilan ta yi tayin akalla Dala dubu 3500 ga kowanne dan Afrika da ke gudun hijira ko ci rani a kasar tare da tikitin jirgi da za a mayar da shi kasar sa ta haihuwa kyauta.
Kafin dakatar da shirin dai Isra'ilan ta yi tayin akalla Dala dubu 3500 ga kowanne dan Afrika da ke gudun hijira ko ci rani a kasar tare da tikitin jirgi da za a mayar da shi kasar sa ta haihuwa kyauta. REUTERS/Nir Elias

Isra'ila ta dakatar da shirinta na korar dubun dubatar bakin haure 'yan Afrika da ke ci rani a kasar ba bisa ka'ida ba. Shirin dai a baya na da nufin mayar da akalla 'yan ci rani dubu 42 kasashensu wadanda galibu suka fito daga Sudan da Eritrea.

Talla

Babban mashawarcin Firamininta Benjamin Netanyahu kan sha'anin doka, ya shaidawa kotun kolin kasar matakin su na dakatar da shirin korar bakin hauren bayan da wasu kasashe suka ki amince da matakin karbar 'yan gudun hijirar.

Tun farko dai jami'an agajin da ke kula da 'yan gudun hijirar sun cimma yarjejeniyar mayar da su kasashen Rwanda da Uganda, sai dai kuma daga bisani sun nuna tirjiya, ko da ya ke dama galibin 'yan gudun hijirar sun ce sun gwammaci zaman yari akan akaisu kasashen biyu ko kuma asalin kasashensu.

Shirin korar 'yan gudun hijirar na Isra'ila dai na shan suka daga bangarori daban-daban ciki har da Majalisar Dinkin Duniya da hukumar da ke kula da 'yan gudun hijira dama kungiyoyin kare hakkin dan adam na ciki da wajen kasar.

A farkon watan Afrilu ne Firaminsta Benjamin Netanyahu ya ce ya dakatar da shirin na fatattakar 'yan gudun hijirar inda ya ce maimakon haka zasu fara aikin mika 'yan ciranin zuwa kasashen Canada Jamus da kuma Italiya.

Hukumar kare hakkin dan adam dai ta jima ta na caccakar matakin da Isra'ilan ke dauka kan 'yan gudun hijirar da kuma bakin haure 'yan Afrika da ke neman mafaka a kasar.

Kafin dakatar da shirin dai Isra'ilan ta yi tayin akalla Dala dubu 3500 ga kowanne dan Afrika da ke gudun hijira ko ci rani a kasar tare da tikitin jirgi da za a mayar da shi kasar sa ta haihuwa kyauta, amma 'yan Afrikan suka bijirewa tsarin, matakin da ya sa ta daura aniyar korar su da karfin tuwo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.