Isa ga babban shafi
Falasdinu

Falasdinu ta bukaci ICC da ta binciki Isra'ila kan laifin yaki

Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riyad al-Malki
Ministan Harkokin Wajen Falasdinu Riyad al-Malki REUTERS/Brendan McDermid

Hukumomin Falasdinu sun bukaci Kotun Hukunta Manyan Laifufuka ta ICC da ta kaddamar da bincike kan abin da suka kira laifufukan yakin da Isra'ila ta aikata wajen kashe Falasdinawan da ba sa dauke da makamai da kuma nuna musu wariyar jinsi.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Falasdinu, Riyad al-Maliki ya bayyana bukatar Falasdinawan bayan ganawar da suka yi ta kusan sa’a guda da babbar mai gabatar da kara ta hukumar ICC, Fatou Bensouda a kotun da ke birnin Haque.

Al-Maliki ya shaida wa manema labarai cewar, matakin yana da matukar muhimmanci da kuma tarihi wajen ganin an yi wa Falasdinawan adalci wajen hukunta Isra'ila wadda ke ci gaba da taka dokokin duniya.

Bukatar ta Falasdinawa na zuwa ne bayan kazamin kisan da sojojin Isra'ila suka yi wa Falasdinawa da ke zanga-zanga ba tare da makamai ba, matakin da ya janyowa Isra'ila suka daga sassan duniya.

Isra'ila ta yi watsi da bukatar ta Falasdinawa wadda ta bayyana a matsayin mara tasiri saboda yadda ba ta cikin kasashen da suka amince da halarcin kotun.

A makon jiya, shugabar masu gabatar da kara Fatou Bensouda ta sha alwashin daukar mataki kan Isra'ila domin kawo karshen munanan matakan da take dauka kan Falasdinawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.