Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

An yi musayar wuta tsakanin Isra’ila da Falasdinu

Wani harin Isra'ila a yankin zirin Gaza
Wani harin Isra'ila a yankin zirin Gaza REUTERS/Amir Cohen

An yi musayar wuta tsakanin bangaren Isra’ila da na Falasdinu, bayan da aka samu labarin kisan wata mata Bafalasdina a yankin kan iyakokin kasashen biyu

Talla

Isra’ila dai na zargin kungiyoyin Hamas da Fatah ne da taimaka wa Falasdinawa a hare-haren Roka da ke fita daga yankin Falasdinu zuwa bangaren Isra’ila.

Dakarun Isra’ila sun ce harin da suka kai ta jirgin sama ya dirar wa wani gungun Falasdinawa da ta kira Sojin sa kai na yankin zirin Gaza ne, bayan wani shirin tsagaita buda wuta da aka cimma sakamakon kisan gilla mafi muni da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa tun bayan shekarar 2014.

Daman dai Isra’ila na cewar tana hararan wasu killatattun gine-gine guda biyu ne, na abinda ta kira ‘yan ta’addan kungiyar Hamas ta Falasdinu da ke a Gaza ne, da suka hada da wasu wuraren kera makamai.

Watsuwar tashin hankali tsakanin kasashen biyu ya zo ne sa’o’I kalilan bayan wani harin da Isra’ila ta kai wa Falasdinawa da dama a wani wurin jana’iza.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai hare-haren da Isra’ila ke ikrarin an kai mata ne daga bangaren Falasdinu.

Tun a ranar 30 ga watan maris ne Falasdinawa suka kaddamar da bore don neman dawo masu da yankunansu da Isra’ila ke ci gaba da mamayewa tun daga shekarar 1948 a lokacin yakin da ya barke a tsakanin bangarorin biyu akan filayen da a yau suna a cikin yankin Isra’ila ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.