Isa ga babban shafi
Amurka

Mai baiwa shugaba Trump shawara ya samu bugun Zuciya

Babban mai baiwa shugaba Trump shawara akan tattalin arziki Larry Kudlow
Babban mai baiwa shugaba Trump shawara akan tattalin arziki Larry Kudlow REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa mai bashi shawara kan harkokin tattalin arziki Larry Kudlow ya samu cutar bugawar zuciya.

Talla

Yanzu haka dai ana kula da shi a wata Asibiti da ke wajen birnin Washington na Amurka, bayan da aka kwasheshi a rigingime cikin wani hali na rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Bugun zuciyar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Kudlow ya zargi Fira ministan Canada Justin Trudeau da dabawa Amurka wuka a baya, wajen taron kasashe 7 da suka fi karfin tattalin arzikin da aka kamala a karshen mako.

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ta kafar twitter ya ce Larry Kudlow da ke aiki tukuru wajen harkokin kasuwanci da tattalin arziki ya gamu da bugun zuciya kuma ana kula da shi a Cibiyar kula da lafiyar Walter Reed.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.