Isa ga babban shafi
Amurka-Korea

Mai yuwa Amurka ta janye wa Korea ta Arewa Takunkumi

Wakilan Amurka da Korea ta Arewa
Wakilan Amurka da Korea ta Arewa SAUL LOEB / AFP

Amurka ta ce janye takunkuman karya tattalin arziki da ta kakaba wa Koriya ta arewa, ya dogara ne ga irin sakamakon da aka cimma a ganawar Donald Trump da kuma Kim Jong Un.

Talla

Babban abin da ake dako daga wannan ganawa tsakanin Donald Trump da kuma Kim Jon Un shi ne ko Koriya ta Arewa za ta amince ta lalata makamanta na nukiliya ko kuma akasin haka

Sakataren wajen Amurka ya ce ba wani abin fargaba matukar dai Koriya ta amince ta lalata makamanta na nukilya, domin kuwa Amurka za ta tabbatar da tsaron kasar a cewarsa.

Ga alama dai kasashen biyu na da kyakkyawan fata dangane da wannan ganawa, musamman lura da yadda aka tsara ta a cikin gaggawa da kuma tafiye-tafiyen da manyan jami’an kasashen biyu suka yi kafin wannan haduwa da ke gudana a kasar Singapore.

Shugaban Amurka ya bayyana matsayinsa dangane da haka, matukar dai kasar ba ta cika sharuddan da aka gindaya ma ta ba, to ba wani sauyin da za a sama a fagen tattalin arziki ko kuma takunkumai.

Wannan ne ya sa muka bayyana cewa da farko dole ne kasar ta amince da kwance damararta, sai a dakata domin ganin abin da zai faru bayan tattaunawar da za a yi wannan talata tsakanin Kim Jon Un da kuma Donald Trump.

Ina da yakinin cewa za a cimma matsaya a tsakaninsu, amma dai yana da kyau mu sani cewa mutanen biyu ne kawai za su iya daukar matakin karshe ko kuma samar da sakamon a lokacin wannan ganawar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.