Isa ga babban shafi
MDD

Gutteress ya soki Trump kan raba yaran 'yan cirani da Iyayensu

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress. AFP

Babban magatakarda na Majaisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kakkausar suka ga matakin raba iyaye da ‘yayansu da gwamnatin Amurka ke kan aiwatarwa akan wadanda suka shiga kasar ba a kan ka’ida ba.

Talla

Antonio Guterres ya ce bakin haure da kuma ‘yan gudun hijira na bukatar kulawa tare da ba su kariya irin wadda ta dace da dokokin kasa da kasa, sabanin abinda gwmanatin Amurka ke yi na raba su da iyalensu.

Stephane Dujarric, mai magana da yawun Guterres, ya ce raba bakin hauren da kuma iyayensu, lamarin da ke kara jefa su a cikin halin kunci da takura.

Daga lokacin da gwamnatin Donald Trump ta fara aiwatar da wannan mataki a cikin makonni 6 da suka gabata, akalla yara kanana 2.000 ne aka raba da iyayensu inda aka tsare wasu a wani sansani na musamman da aka gina cikin barikin sojin jihar Texas, yayin da aka tasa keyar sauran zuwa iyakar kasar da Mexico.

A jiya litinin ma dai shugaban na Amurka Donald Trump ya jaddada cewa kasar ba za ta taba kasancewa matattarar ‘yan ci rani ba, inda ya bayar da umurnin kafa rundunar sojin sama ta musamman da za ta yi sintiri domin kange bakin daga iyakokin kasar na ruwa da kuma tudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.