Isa ga babban shafi
Faransa

Macron da Fafaroma za su zanta kan matsalar baki a Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Christian Hartmann

Shugaban Faransa Emmanuel Macron zai gana da Fafaroma Francis a Fadar Vatican, in da ake saran za su tattauna kan matsalar kwararar baki a Turai, sannan kuma ya karbi wata lambar girma da aka saba bai wa shugabannin Faransa tun karni na 15.

Talla

Shugabannin Faransa da suka gabaci Macron da suka hada da Francois Mitterand da Francois Hollande duk sun ki karbar lambar a yunkurinsu na nesanta kan su da addini.

Mitterand da Hollande sun ki karbar lambar ce don mutunta dokokin da jam’iyyarsu ta Republican ta shata da ke hana wani shugaba nuna bangaranci musamman a kan al’amurran da suka jibanci addini.

Shugaba Macon ya bukaci karfafa dangantaka tsakanin gwamnati da Majami’ar Katolika, matakin da wasu masharhanta ke kallo a matsayin yunkurin warware akidar gwamnatin Faransa ta nesanta kanta wajen yin katsalandar a cikin al’amurran addini.

A shekarar 1905 ne mahukuntan kasar suka raba batutuwan addini da na gwamnati, matakin da ake ganin an dauka ne saboda taka-tsan-tsan musamman idan aka yi la’akari da tarihin yadda Sarakuna na Katolika su ka yi mulikin mulaka’u  fiye da shekaru 200  da suka gabata a Faransa kayin juyin-juya hali ya raba su da mukamansu.

Rahotanni sun ce, shugaba Macron tun yana dan karami yake danganta kansa da darikar Katolika, kafin daga bisani ya fara janye wa lokacin da ya zama matashi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.