Isa ga babban shafi
Iraqi

Iraqi na neman hanyar rabuwa da 'ya'yan 'yan ta'adda

Gwamnatin Iraqi na neman kai da 'ya'yan mayakan kasashen ketare da take tsare da su a gidan yari
Gwamnatin Iraqi na neman kai da 'ya'yan mayakan kasashen ketare da take tsare da su a gidan yari Reuters

Kasar Iraqi ta nemi gwamnatocin kasashen mayakan da take tsare da su saboda  ayyukan ta'addanci da su zo su tattara dururuwan ‘ya’yan mutanen da ake tsare da su a gidan yari don komawa da su kasashen iyayensu na asali.

Talla

Kananan yara akalla 833 wadanda iyayensu suka fito daga kasashen duniya 14 ake ajiye da su a gidajen yarin kasar, kamar yadda ofishin rundunar hadin-guiwa da ke 

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Waje na Iraqi, Ahmed Mahjoub ya bayyana cewa, sun aike wa dukkan ofisoshin jakadancin kasashen da ke Iraqi wannan sako saboda su zo su gabatar da kansu kafin kwashe ‘ya’yan mayakan.

A cewarsa, wadannan kasashe sun hada da Jamus da Azerbaijan da Rasha da sauran kasashen duniya.

Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta duniya na cewa, karkashin dokokin Iraqi ba a hukunta yara masu shekaru kasa da 9, kodayake ana iya daure yara har na tsawon shekaru 5 a gidan yari saboda shiga kungiyar IS.

Wata majiya da ke Rasha na fadin cewa, gwamnatin na kokarin kwaso yaran kasarta, amma kuma babbar matsalar ita ce, babu yaron da ke da wani takardar shaidar in da ya fito.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.