Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Trump ya kare Rasha kan zargin da Amurka ke mata

Kafin su gudanar da taron na kasar Finland dai Donald Trump ya zargi hukumomin liken asirin amurka da taka muhimmiyar rawa wajen haddasa tabarbarewar alaka tsakaninsu da Rasha.
Kafin su gudanar da taron na kasar Finland dai Donald Trump ya zargi hukumomin liken asirin amurka da taka muhimmiyar rawa wajen haddasa tabarbarewar alaka tsakaninsu da Rasha. REUTERS/Leonhard Foeger

Shugaba Donald Trump ya kare Rasha daga zargin da ake yi mata na yin kutse a zaben shugabancin Amurka, na shekarar 2016, wanda yayi nasara kan abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton.Trump ya kare Rasha ne jim kadan bayan Ganawarsa da shugaban kasar Vladmir Putin na kasar Finland.

Talla

Taron tsakanin Vladmir Putin da Donald Trump ya gudana ne kwanaki kalilan bayan da masu gabatar da kara a Amurka suka samu wasu jamián Diflomasiyyar Rasha 12, da laifin satar wasu bayanan sirri na jamíyyar adawa Democrats domin taimakawa Trump wajen samun nasara akan Hillary Clinton.

Bayan shafe awanni biyu shugabannin na tattaunawa ne, Trump ya ce tabbas ya aminta da bayanan shugaba Putin na cewa Rasha ba ta yi kutse cikin zaben shugabancin Amurka domin taimaka mishi wajen samun nasara ba.

Bayanin na Shugaba Trump ya ci karo da wanda hukumomin liken asirin Amurka suka fitar bayan shafe tsawon lokaci suna gudanar da bincike, inda suka bada tabbacin cewa ko shakkah babu Rasha ta sa hannu cikin zaben kasar.

Kafin su gudanar da taron na kasar Finland dai Donald Trump ya zargi hukumomin liken asirin amurka da taka muhimmiyar rawa wajen haddasa tabarbarewar alaka tsakaninsu da Rasha,baya ga takkadamar da ta shiga tsakanin kasashen biyu kan rikicin kasar Ukraine a 2014 da kuma yakin kasar Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.