Isa ga babban shafi

"Ci gaba da amfani da man fetur hadari ne babba ga muhalli"

Kauyen Badswat da ke fuskantar nutsewa cikin ambaliyar ruwa,  sakamakon narkewar katafariyar kankarar lardin Gilgit-Baltistan a kasar Pakistan. 27 ga watan Yuli, 2018.
Kauyen Badswat da ke fuskantar nutsewa cikin ambaliyar ruwa, sakamakon narkewar katafariyar kankarar lardin Gilgit-Baltistan a kasar Pakistan. 27 ga watan Yuli, 2018. Reuters/Peer Muhammad

Wani Binciken masana yanayi ya bayyana bukatar kawo karshen amfani da man fetur, da kuma rungumar sabbin dabarun samun makamashi domin kawo karshen yadda ake gurbata muhalli, da kuma samun yanayi mai zafi a duniya.

Talla

Masanan sun ce, muddin aka cigaba da narkar da kankarar dake samar da sanyi da kuma kona daji kana da fitar da hayakin dake gurbatamuhalli kamar yadda akeyi kowacce shekara, duniya zata fuskancin matsalar da bata taba gani ba wajen samun zafi.

Masanan daga Jami’ar Copenhagen da Jami’ar Australia da kuma Cibiyar gudanar da binciken yanayi dake Jamus duniya na fuskantar barazanar samun munanan ambaliya, da kuma ruwa da iskar dake illa ga jama’a nan da shekaru maus zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.