Isa ga babban shafi
Colombia-Venezuela

Kalubalen da ke gaban Ivan Duque sabon shugaban Colombia

Sabon shugaban kasar Colombia Ivan Duque bayan rantsuwar kama aiki a ranar Talata 7 ga watan Agustan 2018.
Sabon shugaban kasar Colombia Ivan Duque bayan rantsuwar kama aiki a ranar Talata 7 ga watan Agustan 2018. Fabian Ortiz/Courtesy of Colombian Presidency/Handout via REUTER

Sabon shugaban kasar Colombia Ivan Duque ya karbi rantsuwar fara aiki a dai dai lokacin da kasar ke fuskantar tsamin alaka da makociyarta Venezuela baya ga kalubalen da ke gabansa na ganin ya sasanta tsakaninsa da kungiyar ‘yan tawayen kasar FARC.

Talla

Shugaba Ivan Duque mai shekaru 42 a duniya wanda zai maye gurbin Juan Manuel Santos ana ganin abu ne wuya idan bai warware yarjejeniyar zaman lafiyar da magabacinshi ya kulla da ‘yan tawayen FARC ba, la’akari da yadda tun farko ya kalubalanci yarjejeniyar wadda ta kawo karshen rikicin kasar na fiye da shekaru 50.

Duque wanda tsohon lauya ne kuma tsohon dan majalisar dattijan kasar, babban aikin da ke gabansa shi ne ganin ya yi yaki da safarar miyagun kwayoyi da ta ta’azzara a kasar, baya ga daukar matakan ganin ya gyara alakar da ke tsakanin Colombia da makotanta musamman Venezuela.

Nasarar Doque wadda ta ta’allaka kan alakarsa da tsohon shugaba Alvaro Uribe da ya jagoranci kasar daga 2002 zuwa 2010 ya fito kiri-kiri ya nuna adawarshi kan yarjejeniyar da Santos ya cimma da ‘yan tawayen na FARC.

Haka zalika shi ma Doque a jawabin sa na watan Yuni bayan nasarar zabe ya jaddada cewa zai gudanar da wasu gyare-gyare a yarjejeniyar ta Santos.

Sai dai rantsuwar kama aikin na Doque na zuwa ne a dai dai lokacin bangarorin adawa da suka sha kaye a zaben kasar ke gudanar da zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.