Isa ga babban shafi
Amurka-California

Wutar dajin California na ci gaba da watsuwa sassan birnin

Kawo yanzu dai wutar dajin ta hallaka akalla mutane 11 yayinda aka sauya salon kashe ta zuwa amfani da manyan jirage masu feso ruwa.
Kawo yanzu dai wutar dajin ta hallaka akalla mutane 11 yayinda aka sauya salon kashe ta zuwa amfani da manyan jirage masu feso ruwa. REUTERS/Fred Greaves

Dubun Dubatar masu aikin kashe gobara ne yanzu haka ke can na ci gaba da yaki da wutar dajin da ke yaduwa a sassan birnin California na kasar Amurka, bayan da wutar ta hallaka akalla mutane 11 kuma kawo yanzu aka gaza shawo kanta. 

Talla

Rahotanni sun ce wutar wadda ta ke ci da harsuna da yawa ta lakume eka 290,000 yanzu haka, wanda ya kai girmar birnin Los Angeles, a cikin makwanni biyu kacal.

Masu aikin kashe gobara dubu 14 da wadanda aka dauko daga kasashen Australia da New Zealand ne yanzu haka ke ta kokarin kashe gobarar, wadda take ci ba tare da kakkautawa ba.

Cikin abubuwan da ake amfani da su wajen kashe wutar har da jiragen sama masu saukar ungulu da kuma manyan jiragen sama kirar jumbo 747.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.