Isa ga babban shafi
Venezuela

Kotu ta yanke hukuncin dauri zuwa Nicolas Maduro

Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela
Nicolas Maduro,Shugaban kasar Venezuela Reuters

Kotun tsarin mulkin kasar Venezuela, wadda shugaban kasar Nicolas Maduro ya kora saboda bambancin ra’ayi a tsakaninsu, ta yanke hukuncin daurin shekaru 18 akan shugaban kasar saboda samun sa da laifin karbar rashawa.

Talla

Kotun, wadda ta yi zamanta a birnin Bogota na kasar Colombia inda alkalanta ke gudun hijira tun lokacin da shugaba Maduro ya tube su daga mukamansu, ko baya ga hukuncin daurin na shekaru 18, ta kuma ci shugaban kasar tara har sau biyu, ta farko dalar Amurka bilyan 35, sai kuma ta biyu dala bilyan 25.

Shugabar kotun Rafael Rommel-Gil, ita ce ta sanar da wannan hukunci, sannan ta bukaci Maduro ya sauka daga mukaminsa.

Shugabar kotun ta nemi a fitar da sammacin kasa da kasa domin cafke Nicolas Maduro.

Wani na hannun daman shugaba Maduro,Disdado Cabello, ya bayyana hukuncin a matsayin abin dariya, yana mai cewa ta yaya kotun da ke zaune a kasar Colombia za ta yanke hukuncin dauri a kan shugaban Venezuela.

An kafa wannan kotu ce kimanin shekara daya da ta gabata, bayan share tsawon watanni ana zanga-zangar adawa da shugaban kasar, inda aka samu asarar rayukan mutane 125.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.