Isa ga babban shafi
Turkiyya-Amurka

Turkiyya ta yi watsi da bukatar sakin Limamin Kirista dan Amurka

Rashin sakin Limamin Kiristan da Turkiyya ta yi duk da bukatar hakan da Amurka ta yi shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen rura rikicin da kasashen biyu ke fuskanta.
Rashin sakin Limamin Kiristan da Turkiyya ta yi duk da bukatar hakan da Amurka ta yi shi ne ya taka muhimmiyar rawa wajen rura rikicin da kasashen biyu ke fuskanta. ©Demiroren News Agency, DHA via REUTERS

Kotun Turkiyya ta yi watsi da bukatar daukaka karar da Amurka ta shigar don sakin limamin addinin Kiristan ba'amurke Andrew Brunson da kasar ke rike da shi wanda ya haddasa tsamin alaka tsakanin kasashen biyu.

Talla

A zaman kotun na yau Laraba ta yanke hukuncin cewa Turkiyya za ta ci gaba da rike Mr Andrew wanda ake tuhuma da laifuffukan ta'addanci da na leken asiri kuma matukar aka same shi laifi za a yanke masa hukuncin shekaru 35 a gidan yari.

Andrew Brunson wanda hukumomi a Turkiyyan suka kame shi tare da sanya shi a kurkuku tun a shekarar 2016 kafin dawo da shi daurin gida a watan daya gabata saboda dalilai na lafiya, Kotun ta ce zai iya daukaka kara nan da kwanaki 15.

Rike limamin Kiristan da Turkiyya ke ci gaba da yi duk da bukatar Amurka kan sakinsa shi ne ya rura wutar rikicin da kasashen biyu ke fuskanta yanzu haka da ya kai ga tsamin alaka mafi muni da suka taba fuskanta.

Ko a makon da ya gabata ma, Trump ya ninka haraji kan kayakin karafa da Sampolon da Turkiyya ke shigar masa yayinda ita kuma Turkiyyan ta kara haraji kan wasu kayakinta baya ga hana shigowa da wasu kayakin Na'urar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.