Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Amurka ta ce kotun duniya ICJ bata isa ta yi shara'ar dake tsakninta da Iran ba

A cewar Iran matakan dawo da takunkuman ba komi ba ne face yunkurin tagayyara tattalin arzikin kasar.
A cewar Iran matakan dawo da takunkuman ba komi ba ne face yunkurin tagayyara tattalin arzikin kasar. © REUTERS/Lisi Niesner/File Photo

Kasar Amurka ta bayyanawa wa alkalan kuton Majalisar Majalisar Dinkin Duniya cewa, basu da hurumin daukar mataki, kan karar da kasar Iran ta shigar a gaban su, na neman sauke takunkuman da ta kakabawa kasar kan magnar da ta shafi shirinta na Nukliya.

Talla

Iran wadda tuni radadin takunkumin ya fara tasiri a kanta, ta jaddada cewa shugaba Donald Trump ya karya dokor shekarar 1955, kan matakin sake maida takunkumin bayan da aka janye shi sakamakon yarjejeniyar nukiliyar da kasar ta cimma da manyan kasashen duniya cikinsu kuwa har da ita kasar Amrruka

Lauyan gwamnatin Amurka Jennifer Newstead ta shaida wa kutun duniya dake birnin Hague cewa, bata da cancantan sauraren karan ta Iran ba.

To sai dai lauyan Iran ya bayyanawa kutun cewa, takunkumi na barazana ga jin dadin al’ummar kasar tare da haifar da asarar biliyoyin daloli ga kasar ta harkokin kasuwanci.

Gwamnatin Iran ta shigar da kara a kotun duniya da ke birnin Hague don kalubalantar aniyar shugaban Amurka Donald Trump ta sake kakaba mata takunkuman da aka janye mata tun shekarar 2015.

Lauyan gwamnatin Iran Mohsen Mohebi ya shaida wa kotun cewa, matakan na Amurka ba komai ba ne face yunkurin rugurguza tattalin arzikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.