Isa ga babban shafi

Amurka ta yi watsi da hukuncin kotun duniya kan Iran

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo. Tweet@SecPompeo

Amurka tayi watsi da hukuncin kotun duniya na haramta takunkumin karya tattalin arzikin da ta dorawa kasar Iran, yayin da ta sanar da kawo karshen yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla a shekarar 1955.

Talla

Kotun duniyar ta ICJ, ta bukaci Amurka ta cire takunkumin da ta dorawa kasar ta Iran ba tare da bata lokaci.

Yayin mayar da martani kan hukuncin kotun da ya bukaci Amurkan ta janye takunkumin da ta dorawa Iran kan magunguna da abinci, da kuma kayan sufurin jiragen saman fararen hula, sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo yace takunkumin bai shafi kayayaykin jinkai ba.

Saboda haka Sakataren ya bayyana kawo karshen yarjejeniyar kawancen da kasashen biyu suka kulla a shekarar 1955 lokacin da Iran ke karkashin Sarki Sha dake abota da Amurkar.

Pompeo da ya bayyana hukuncin kotun a matsayin wanda ke da nasaba da siyasa da kuma farfaganda, yace matakin da suka dauka kan kasar ta Iran ya dace, saboda tarihinta na tallafawa ayyukan ta’addanci da kera makamai masu linzami da makamantar haka.

A nashi martinin, ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, ya bayyana Amurka a matsayin mara bin doka wajen soke yarjejeniyar da kuma kin bin umurnin kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.