Isa ga babban shafi
Fasaha

"Wayoyin Salula na hana gina yara manyan gobe"

Wasu matasa na bai wa wayoyin salula muhimmanci fiye da koma a rayuwa
Wasu matasa na bai wa wayoyin salula muhimmanci fiye da koma a rayuwa (Photo by Alberto Buzzola/LightRocket via Getty Images)

Wani binciken masana ya ce, wayoyin salular Smartphones da shafukan sada zumunta na illa wajen gina yara manyan gobe.

Talla

Wani Farfesa a fannin halayyar dan Adam a Jami’ar San Diego, Jean Twenge ya ce, yaran da aka haifa daga shekarar 1995 zuwa yanzu, na daga cikin wadanda rayuwarsu ta ta’allaka gaba daya ga wayoyin, in da suke kashe daukacin lokacin da suke da shi wajen ziyarta dandalin sada zumunta da kuma yin wasanni a kan wayar a maimakon mayar da hankali kan karanta litattafai da kuma samu isasshen barci har ma da samun lokacin ziyarar abokai domin tattaunawa kan wasu mas’aloli.

Twenge ya ce, irin wadanan matasa na girma a hankali cikin wannan dabi’a ta bai wa wayoyin salula fifiko a rayuwa, kuma lokacin da za su cika shekaru 18, yana da wuya su samu lasisin tukin mota ko kuma samun aikin da zai rika kawo musu kudaden shiga.

Kazalika matasan ba za su iya dogaro da kansu ba wajen balaguro da yawon bude ido ba tare da iyayensu, sabanin yadda aka saba gani a shekarun baya.

Farfesa Twenge ya bada shawara ga iyaye da su dauki matakin sanya ‘ya’yansu takaita amfani da waya akalla na sa’oi biyu a rana, wanda hakan zai yi matukar taimakawa harkokin rayuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.