Isa ga babban shafi
WHO-LAFIYA

WHO ta koka da karuwar cutar kyanda a sassan duniya

Bayanan hukumar na nuni da cewa ba kadai a Afrika cutar ta tsananta ba, har ma da wasu sassa na Tarayyar Turai.
Bayanan hukumar na nuni da cewa ba kadai a Afrika cutar ta tsananta ba, har ma da wasu sassa na Tarayyar Turai. Mike Blyth/ domaine public

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwar cewar cutar kyanda ta karu da kashi 30 a fadin duniya a shekarar da ta gabata, sabanin yadda take a shekarar 2016.

Talla

Hukumar lafiyar ta Majalisar WHO ta ce cikin kasashen da aka samu karuwar masu kamuwa da cutar harda kasashen Turai da suka hada da Jamus inda ake gudanar da rigakafi sosai.

Sanarwar hukumar ta WHO ta nuna cewa matsalar ta kai wani yanayi na tayar da hankali a fadin duniya, duk da ya ke cewa adadin masu kamuwa da cutar ya saba daga sashe zuwa sashe.

Martine Friede, Daraktan kula da rigakafin hukumar, ya ce cece kucen da masana ke yi kan maganin rigakafin da ake amfani da shi ya yi tasiri ga matsayin da iyaye su ke dauka wajen karbar rigakafin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.