Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka na neman kotu ta daure Michael Cohen shekaru 5 ko 6

Tun a makon jiya, Cohen ya amsa tuhumar da ake masa na sharara karya gaban zaman majalisun Amurka.
Tun a makon jiya, Cohen ya amsa tuhumar da ake masa na sharara karya gaban zaman majalisun Amurka. REUTERS/Andrew Kelly

Masu shigar da kara a Amurka sun bukaci zartas da hukuncin daurin shekaru akalla 5 zuwa 6 ga Michael Cohen tsohon lauyan shugaban kasar Donald Trump bayan tabbatar da cewa ya bayar da cikakkiyar dama ga Rasha wajen yin kutse a zaben kasar na shekarar 2016, batun da ya amsa a gaban kotu.

Talla

Baya ga tuhumar kutsen na Rasha a zaben Amurka, Cohen ya kuma amsa batutuwa masu alaka da damfarar bankuna baya ga wuce makadi da rawa yayin yakin neman zaben Donald Trump a shekarar 2015.

Wasu bayanai masu shafuka 40 da masu shigar da karar suka gabatar gaban Kotu sun tabbatar da yadda tattaunawar Cohen da wakilan Rasha ta gudana kan yadda za ataimakawa Donald Trump tsallake zaben na shekarar 2016.

Tun a makon jiya, Cohen ya amsa tuhumar da ake masa na sharara karya gaban zaman majalisun Amurka, ko da dai Donald Trump ya kira shi da mutum mai rauni wanda ke amsa laifin da bai yi ba don samun sassaucin hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.