Isa ga babban shafi
Duniya

Mujallar Time ta Amurka ta karrama Marigayi Jamal Khashoggi

Fitaccen dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi da aka yi wa kisan gilla a Ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na Turkiyya.
Fitaccen dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi da aka yi wa kisan gilla a Ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santambul na Turkiyya. 法新社/MOHAMMED AL-SHAIKH

Mujallar Time da ke kasar Amurka ta bayyana dan Jaridar Saudi Arabia Jamal Khashoggi da aka yi wa kisan gilla tare da wasu yan Jaridu a matsayin Gwarzayen shekarar 2018.

Talla

Sanarwar da Jaridar Time ta bayar ta nuna cewar, bayan Khashoggi akwai yar Jaridar Philippines Maria Ressa da wakilan Reuters da aka tsare a Myanmar Wa Lone da Kyaw Soe Oo da kuma wakilin Capital Gazzete Annapolis, Maryland tare da wasu yan Jaridu guda 5 da aka kashe a watan Yuni cikin jerin gwarzayen.

Ita dai Jaridar Time da ke da Cibiya a New York na kasar Amurka na bada wannan lambar girmar ce ga mutunen da suka yi fice a duniya.

Jamal Khashoggi dai shi ne fitaccen dan Jaridar Saudiya da ya yi kaurin suna wajen sukar salon mulkin Yarima Mai jiran gado na kasar Muhammad Bin Salman dalilin da ake ganin ya janyo masa kisan gilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.