Isa ga babban shafi
Poland

Kasashe 200 sun gaza cimma matsaya guda kan dumamar yanayi

Zauren dake karbar bakuncin taron wakilan kasashen duniya 200 kan matsalar dumamar yanayi a birnin Kotowice na kasar Poland.
Zauren dake karbar bakuncin taron wakilan kasashen duniya 200 kan matsalar dumamar yanayi a birnin Kotowice na kasar Poland. REUTERS

An fuskanci tsaikon cimma matsaya guda tsakanin wakilan kasashen duniya dake taro kan rage dumamar yanayi a birnin Katowice dake kasar Poland.

Talla

Da farko an tsara kammala tattaunawar kafin safiyar yau ranar Asabar, amma hakan bai yiwu ba, a dalilin gaza cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwa.

Batutuwan sun kunshi, yadda za’a samar da kudaden aiwatar da shirin na rage matsalar ta dumamar yanayi, da kuma kasashen da ya kamata su samar da kaso mafi tsoka daga cikin tallafin.

Abu na uku da wakilan kasashen akalla 200 da ke halartar taron na Poland ke takaddama akai shi ne, zargin da akewa kasashe masu arzikin masa’antu, wajen kin mika tallafin kudaden da suka alkawarta a yarjejeniyar birnin Paris ta 2015, ga kasashen da matsalar ta dumamar yanayin ta fi cutarwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.