Isa ga babban shafi
Turkiya-Faransa

Babu wata riba da Faransa za ta samu a Syria- Turkiya

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron LUDOVIC MARIN / POOL / AFP

Turkiya ta gargadi Faransa cewa, babu wata riba da za ta samu dangane da ci gaba da wanzar da dakarunta da ke bai wa mayakan Kurdawa kariya a Syria.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Turkiya, Mevlut Cavusoglu ya bayyana haka bayan gwamnatin Faransa ta ce, dakarun nata za su ci gaba da aiki a Syria duk da matakin da Amurka ta dauka na janya dakarunta dubu 2 a kasar bayan Donald Trump ya ce, an ci galabar mayakan ISIS, ikirarin da manyan kasashen Turai suka musanta.

Turkiya na kallon mayakan Kurdawa da ke samun goyon bayan Amurka a matsayin ‘yan ta’adda, yayin da shugaba Recep Tayyip Erdogan ya jinjina wa shugaba Trump kan matakin janye dakarun.

Turkiyya ta sha alwashin murkushe kungiyar IS da sauran kungiyoyin da ke dauke da makamai ciki har da na Kurdawa.

A bangare guda, shugaba Erdogan ya gayyaci Trump domin ya ziyarci kasar Turkiyya cikin shekara mai zuwa, kamar dai yadda sanarwa daga fadar shugaban na Amurka ta tabbatar.

Gayyatar na zuwa ne bayan tattaunawa ta wayar tarho a tsakanin shugabannin biyu, wadda a karshenta ne Trump ya sanar da matakin janye sojojin na Amurka daga Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.