Isa ga babban shafi
Amurka

Farin jinin Trump ya zube a idon Amurkawa

Shugaba Donald Trump na Amurka
Shugaba Donald Trump na Amurka REUTERS/Yuri Gripas

Wata kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna cewa, Amurkawa sun koka da shekaru biyu na mulkin shugaba Donald Trump wanda farin jininsa ya zube a idonsu sakamakon matakan da yake dauka a fannoni da dama musamman a fannin tattalin arziki da hulda da kasashen duniya. 

Talla

Rahoton binciken jin ra'ayoyin jama'ar da tashoshin labarai na ABC da kuma Washington Post suka fitar na cewa, farin jinin shugaba Trump ya zube kasa warwas musamman bayan takardamar da aka samu na rufe baitulmalin gwamnatin kasar.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaba Trump ya jingine tsattsauran ra'ayin ci gaba da rufe wasu ma'aikatun gwamnatin kasar duk da cewa, Majalisar Wakilai karkashin Jam'iyyar Democrat ba ta amince da bukatarsa ta ba shi Dala biliyan 5.7 ba domin gina katanga akan iyakar kasar da Mexico.

Sabuwar kididdigar jin ra'ayoyin Amurkawan na nuna  cewa, Trump ya rasa samun tagomashin da ake bukata a kasar.

Game da tattalin arziki da Trump ke kurarin samun nasara kuwa, rahoton na cewa kashi 49 daga cikin Amurkawa na cewa ya yi abin azo-a-gani, amma kuma kashi 61 da ke sa ran ganin ya yi nasara na ta cizon yatsa.

A bangaren samar da guraben aiki kuwa, masu hasashen cewa, shugaban zai samu nasara, sun janye hasashensu.

An hada rahoton ne tsakanin ranakun Litinin da Alhamis na makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.